<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Ya Allah Uba, Ga Ni Nan LW167</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ya Allah Uba, ga ni nan,
 Ba kai ne ka kira ni ba?
 Mai yalwar jinƙai, yafe ni,
 Na zo, na zo, ka cece ni.

[V2]
 2) Ya Yesu, kai mai iko ne,
 Alheri, ceto naka ne.
 Sai ka ji kukana yanzu,
 Na zo, na zo, Mai Cetona.

[V3]
 3) Ya Ruhun gaskiya, Ruhun rai,
 Ni ne na bata zuciyarka.
 A cikin rashin ƙarfina
 Na zo, na zo, ka cika ni.

[V4]
 4) Ubangiji, Almasihu,
 Ƙaunarka ce ta jawo ni,
 Ba za ka ƙi mai sonka ba,
 Na zo, na zo, ka karƃe ni.</lyrics>
<hymn_number>167</hymn_number>
</song>